Labarai
Rundunar Sojin kasar nan ta hallaka aƙalla ‘yan ta’adda 60 a Borno

Rundunar Sojin kasar nan ƙarƙashin Operation Hadin Kai sun hallaka aƙalla ‘yan ta’adda 60 a wani gagarumin farmaki da suka kai wa Boko Haram a garin Bita da ke jihar Borno.
Bayanin nasarar dai na kunshe ne a cikin wani sako da rundunar sojin kasar nan ta wallafa a shafin ta na X.
Rundunar ta ce farmakin wanda ya haɗa da hare-haren ƙasa da na sama, an gudanar da shi da tsakar dare, wanda ya janyo mummunan hasara ga ‘yan ta’addan.
Harin ya biyo bayan bude wuta da ‘yan ta’addar suka yi, inda sojoji suka mayar da martani, tare da samun taimakon jiragen yakin A-29 Super Tucano da Dragon, waɗanda suka yi luguden wuta kan ‘yan ta’addan.
Bayan artabu mai tsanani da ya ɗauki kusan sa’o’i biyu da rabi, rahotanni sun tabbatar da cewa an kashe aƙalla ‘yan ta’adda 60, tare da lalata motocin su biyu da ke ɗauke da bindigogi.
You must be logged in to post a comment Login