Labarai
Rundunar sojin Najeriya za ta dauki sabbin jami’ai 24,000

Rundunar sojin ƙasan Najeriya, ta bayyana sabuwar aniya ta ɗaukar sojoji 24,000 aiki domin ƙara ƙarfin aiki da inganta shirin yakar kalubalen tsaro.
Wannan sanarwar ta fito ne daga bakin shugaban rundunar sojin Laftanar Janar Waidi Shuaibu, yayin ziyarar aiki da ya kai jihar Kaduna.
Zagazola Makama kwararre a fannin tsaro, ya wallafa a shafin X cewa Waidi Shuaibu ya yi bayanin cewa sababbin cibiyoyin horo uku da shugaba Bola Tinubu ya amince da su za su bada damar inganta aikin Dakarun soji.
Ya ce, yawan yankunan da sojoji ke aiki a cikinsu da kuma yanayin barazanar tsaro ya sanya buƙatar karin sojoji ta zama wajibi.
Shugaban rundunar ya ce, sabon shirin horon zai mayar da hankali ne kan kwarewar zamani da dabarun yaki domin tabbatar da cewa rundunar tana da ma’aikata masu inganci da kwarewa.
Ya bayyana cewa bayan karin adadin jami’ai, shirin zai ƙara inganci da ƙwarewar aiki ta fuskar dabarun yaƙi da ɗaukar mataki cikin gaggawa.
You must be logged in to post a comment Login