Labarai
Rundunar sojin sama kasar nan ta tura jiragen yaki kirar jet guda 100 don bincike daliban Dapchi
Rundunar sojin saman kasar nan ta tura da jiragen saman yaki kirar jet guda dari domin binciko ‘yan matan sakandaren Dapchi da ‘yan Boko-Haram su ka sace su ka kuma yi garkuwa da su a baya-bayan nan.
Ministan yada labarai Alhaji Lai Muhammed ne ya bayyana haka ta cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai jiya a Abuja,
Sanarwar ta ce ashirin daga cikin jiragen sun yi shawagin tsawon awanni dari biyu cikin mako guda.
Alhaji Lai Muhammed ta cikin sanarwar dai, ya kuma ce tuni babban hafsan sojin saman kasar nan Air Marshall Sadique Abubakar ya koma jihar Yobe da zama a ci gaba da binciken ‘yan matan na Dapchi.