Connect with us

Labarai

Jiragen yaki za su iso Najeriya -Rundunar sojan sama

Published

on

Rundunar sojan saman kasar nan zata karbi sabon jirgin shalkwafta da za’a yaki ‘yan ta’adda da shi kirar Mi-17IE  ranar Alhamis 6 ga watan nan da muke ciki a dandalin Eagle dake babban birnin tarayya Abuja.

Wannan na kunshe cikin sanarwar da daraktan yada labarai na rundunar Air Commodore Ibikule Daramola ya fitar a jiya  Lahadi cewar, rundunar zata yi atisaye kafin da bayan karbar jirgin, kasancewar yana daya daga cikin horon sanin makamar aiki na sabon jirgin ga sojojin sama.

har ila yau, sanarwar ta ce  za’a fara Atisayen ne daga yau Litinin 3 ga wata zuwa  ranar Alhamis 6 ga wata.

A cewar sanarwar za’a gudanar da bikin ne cikin ‘yar  kwarya kwarya ba tare an kashe wasu magundan kudade ba.

Zamfara:Jiragen yakin rundunar sojin sama sun fara luguden wuta

Rundunar sojin sama kasar nan ta tura jiragen yaki kirar jet guda 100 don bincike daliban Dapchi

Shugaba Buhari ya kaddamar da sabbin jiragen shalkwabta guda 2

Sanarwar ta kara da cewar, a don haka kada al’umma su firgota kasancewar za’a ga jiragen  na shalkwata na shawagi a sararin sama.

Ka zalika idan za’a iya tunawa Najeriya ta karbi sabbin jiragin shalkwata guda 2 na yaki a ranar 29 ga watan Afirilun bara  kafin bikin ranar ‘yan cin kai  da aka yi a Abuja.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 333,103 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!