Labarai
Rundunar Sojin sama ta biya diyya ga mutanen ƙauyukan Gidan Bisa da Rumtuwa

Rundunar Sojin Saman Nijeriya ta ce ta biya diya ga mutanen ƙauyukan Gidan Bisa da Rumtuwa, a Karamar Hukumar Silame ta jihar Sokoto bayan wani harin jirgin sama da aka yi bisa kuskure a jihar.
Rundunar ta ce harin ya faru ne a yayin wani aiki na tsaro, amma daga baya aka gano cewa an kai harin ne ga mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.
A cewar ta biyan diyyar na nufin tausayawa da rage raɗaɗi ga iyalan waɗanda abin ya shafa, tare da alƙawarin cewa za a ƙara tsaurara matakan aiki domin hana sake faruwar irin wannan kuskure.
Lamarin ya faru ne a Ranar 25 December shekarar da ta gabata inda fararen hula 13 suka rasa rayukansu.
You must be logged in to post a comment Login