Labarai
Rundunar soji sun dakile wani mummunan hari a jihar Plateau

Rundunar sojin kasar nan sun dakile wani hari da ake zargin ’yan ta’adda ne suka kai a ƙaramar hukumar Shendam ta Jihar Plateau. Rahotanni sun ce lamarin ya faru da misalin ƙarfe 7:30 na safe a yankin kasuwar shanu ta Yelwa, bayan samun kiran gaggawa kan harbe-harbe da aka ji.
Ta cikin wani rahoto da shafin Zagazola Makama ya fitar an ce sojojin sun garzaya wurin da sauri, lamarin da ya sa maharan suka tsere zuwa cikin daji. Bayan haka, an gano wasu mutane biyu da suka jikkata sakamakon harbin bindiga, inda aka kai su asibiti domin samun kulawa, yayin da ake ci gaba da farautar waɗanda suka tsere.
Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan wani hari da ya yi sanadin mutuwar mutane kusan 28 a yankin Jos ta Arewa, wanda ya jefa al’ummomi cikin fargaba. Hakan ya sa gwamnatin Jihar Plateau ta sanya dokar hana fita na awanni 48 domin kwantar da hankula.
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya jajanta wa iyalan waɗanda abin ya shafa, yana mai tabbatar da cewa za a hana sake aukuwar hakan a nan gaba.
You must be logged in to post a comment Login