Labarai
Rundunar Yan Sanda na fama da matsalar masu yada labaran karya-Kayode Egbetokun

Sifeto janar na Yan Sandan Najeiya Kayode Egbetokun, ya ce, babu wata hukuma a fadin Najeriya da ke fuskantar mummunan tasiri daga labaran karya kamar ta ‘yan sanda.
Kayode Egbetokun ya bayyyana hakan ne a taron hulda da Jama’a da aka shirye a Abuja, inda ya ya bukaci jami’an hulda da jama’a su rika amsa kira cikin gaggawa a duk lokacin da labarai marasa tushe suka bayyana.
Haka kuma, ya kara da cewa jami’an su shirye suke su yi aikin sintiri, kan sahihan bayanan don kai dauki, da haɗin gwiwa da jama’a da ‘yan jarida wajen kare mutuncin aikin hukumar a kasa.
You must be logged in to post a comment Login