Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Nadin kayode egbetokun an ajiye kwarya a gurbinta- Sarkin Kano

Published

on

Mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero,ya bayyana mukamin da shugaban kasa bola Ahmad tunibu ya bawa kayode egbetokun a matsayin mai rikon mukamin sufeton yan sanda na kasa da cewa ya cancanta duba da irin gogewar da yasamu a fannin aikin yan sanda Wanda hakan zai bashi damar ciyar da kasa gaba.

Sarkin yace yan sanda na taka gagarumar rawa wajen gani sun kare rayuka da dukiyoyin al’umma, dan haka sai ya hori mai rikon mukamin na sefotan yan sanda da yaji tsoron Allah a dukkanin ayyukansa tare da tabbatar masa da goyan bayan masarautar Kano a kowanne lokaci.

Mai rikon mukamin sufeton yan sandan na kasa kayode egbetokun ya tabbatar da cewa rundunarsu a shirye take wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma inda yabukaci hadin kan masauratar dama sauran masu rike da sarautu a fadin kasar nan.

Ya kuma shaidawa Mai martaba sarki cewa yazo Kano ne don halartar bikin yaye yan sanda da za’a gudanar a makarantar horar da yan sanda ta wudil wato wudil police Academic.

Freedom radio ta rawaito cewa shugaban yan sanda na kasa IG kayode yace ya kawowa fadar Kano ziyara ne don neman tabarrakin sarki da kuma shawarwarinsa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!