Connect with us

Kiwon Lafiya

Rundunar ‘yan sanda ta kammala shiri don bada tsaro yayin gudanar da zabe

Published

on

Rundunar ‘yan sandan Najeriya nan ta ce, ta shirya tsaf domin bada tsaro a jihohin Kano da Katsina da kuma Jigawa a yayin zabukan gwamnoni da na ‘yan majalisun dokokin da za a yi a gobe Asabar.

Mataimakin sufeta janar mai kula da jihohin Kano da Katsina da kuma Jigawa AIG Danbature ne ya bayyana haka ta cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in yada labaran rundunar shiyya ta daya da ke nan Kano, DSP Sambo Sokoto.

Sanarwar ta ce rundunar ta gama shirin ta wajen tabbatar da tsaro a dukkannin lunguna da sakuna na jihar Kano don ganin an yi zaben cikin koshin lafiya.

A cewar sanarwar rundunar za ta yi aiki tare da sauran jami’an tsaro wajen tabbatar da ckakken tsaro yayin zabukan.

DIG Danbature ta cikin sanarwar dai, ya kuma gargadi masu neman ta da zaune tsaye yayin zabukan da su guji yin hakan domin a shirye suke su hukunta duk wani da aka kama yana neman ta da hatsaniya a lokacin zaben ko bayan zabe.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!