Connect with us

Kiwon Lafiya

Rundunar ‘Yan sanda ta kubutar da ‘Yan Afrika ta Kudu biyu da aka sace su a Kaduna

Published

on

Rundunar ‘Yan sandan Najeriya ta ce ta kubutar da wasu ‘Yan kasar Afrika ta Kudu biyu da aka sace su a wani wurin aikin hakar ma’adinai cikin kauyen Maidaro a jihar Kaduna.

Wata sanarwa da mai Magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jimoh Mashood ya fitar, ta ce sai da jami’an tsaro suka yi amfani da jirgi mai saukar Ungulu da wasu ‘yan sanda na musamman kafin cimma sako mutanen guda biyu.

Mutanen da aka kubutar sun hada da Thomas Arnold Pearce da Mista Hendrik Gideon bayan sace su a ranar Talata 23 ga watan Janairun da muke ciki  a kauyen Maidaro.

Sanarwar kuma ta ce an sako mutanen ne a jiya Asabar  ba tare da wani rauni a jikin su ba.

Sai dai rundunar ‘yan sandan ba ta yi bayani ba ko sai da aka biya kudin fansa kafin a sake su.

Al’amarin dai na zuwa ne kasa da mako guda bayan kubutar da wasu turawa ‘yan Amurka biyu da kuma ‘yan Canada biyu da aka sace a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,694 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!