Labarai
Rundunar Yan sandan Anambra ta cafke matasa 2 da ake zargi da satar mutane

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Anambra ta kama wasu matasa biyu da ake zargi da aikata laifukan garkuwa da mutane da kuma fashi da makami, a garin Umudioka da ke karamar hukumar Dunukofia.
Rundunar, ta cikin haka ne ta ikin wata sanarwa da mai magana da yawunta DSP Tochukwu Ikenga ya fitar.
Sanarwar ta ce, an samu nasarar kama matasan da ake zargi ne biyo bayan samun bayanai daga wata mata da ta kubuta bayan da suka yi garkuwa da ita a baya-bayan nan.
Wadanda aka kama din sun hada da Onele Solomon wanda aka fi sani da Federal da Simeon Chidera wanda shi kuma aka fi sani da Chaplet, dukkansu ‘yan shekaru 23.
Haka kuma, Sanarwar ta kara da cewa da zarar an kammala bincike za a gaggauta mika wadanda ake zargi gaban kotu domin daukar mataki na gaba.
You must be logged in to post a comment Login