Kaduna
Rundunar Yan sandan Jahar Kaduna ta gayyaci tsohon gwamna El-rufa’i

Rundunar ‘Yan sandan jahar Kaduna ta gayyaci tsohon Gwamnan jihar, Nasir El-Rufa’i da sauran jagororin jam’iyyar ADC kan zargin yunkurin tayar da zaune tsaye.
Hakan na kunshe ne a cikin wata wasika da ke dauke da kwanan watan hudu ga wannan watan nan, da sa hannun mataimakin kwamishinan yan sanda mai kula da sashen binciken manyan laifuka Uzairu Abdullahi.
Wasikar ta bayyana cewa, ta na bincike a kan zargin hada baki da tunzura alummar gari, da tayar da hargitsi.
A makon da ya gabata ne aka yi musayar yawu tsakanin Gwamnatin jahar Kaduna, da tsohon Gwamnan kan wasu ’yan daba da suka kai wa taron jam’aiyyar ADC hari a jahar, sannan suka jikkata wasu mahalarta taron.
You must be logged in to post a comment Login