Labarai
Rundunar Yan sandan Kano ta cafke Mu’azu Barga da ake zargi da fashi da haddasa fadan Daba

Rundunar ’Yan Sandan Kano ta cafke wani riƙaƙƙen ɗan daba da ake nema ruwa a jallo, mai suna Mu’azu Barga, bisa zargin aikata fashi da makami da haddasa rikice-rikicen Daba a unguwar Sheka.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook a daren jiya Lahadi.
Ya ce jami’an sashen yaki da Daba na rundunar ne suka kama Barga bayan dogon bincike da kuma koke-koke daga al’umma game da laifukan da ake zarginsa da aikatawa.
You must be logged in to post a comment Login