Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yan Sanda a Kano sun cafe yan daba yayin da suke tada rikici

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano, ta ce, ta cafke wasu yan Daba da sanyin safiyar Talatar nan da muke ciki.

Rundunar ta cafke matasan su bakwai ne yayin da suke tsaka da fafata wani rikicin Daba
a tsakanin wasu bangarori guda biyu a kusa da kasuwar Rimi.

Mai magana da yawun rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a daren ranar Talata.

Ya ce, bayan samun rahoton barkewar rikicin tsakanin bangarorin ‘yan Daban, kwamishinan ‘yan sanda Kano Muhammad Hussain Gumel, ya bada umarnin aika jami’an rundunar inda suka samu nasarar cafke wasu daga cikinsu.

Jami’in ya kara da cewa, rundunar ba za ta saurara wa duk wanda ya ke kokarin haddasa fitina ba a fadin jihar Kano.

 

Rahoton: Abdulkarim Muhammad Tukuntawa

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!