Labarai
Rundunar yan sandan Kano ta gurfanar da matasa 333 da ta kama yayin zaben cike gurbi a Kotu

Rundunar yan sandan jihar Kano, ta gurfanar da matasa 333 da aka kama yayin zaben cike gurbi a gaban kotunan majistire da ke Gyadi-Gyadi da kuma Nomansland.
kwamishinan ’yan sandan Kano Ibrahim Adamu Bakori, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai a yau Litinin.
Ya ce, an kama makamai iri-iri a hannun matasan ciki har da wadanda aka samu da bindigogi da wukake da layu da takardun kuri’ar zabe da akwatunan zabe da kuma kuɗi sama da naira miliyan huɗu.
Haka kuma Kwamishinan yan sandan na Kano Ibrahim Adamu Bakori, ya nemi haɗin kan al’ummar Kano wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro.
You must be logged in to post a comment Login