Labarai
Rundunar yan sandan Kano ta haramta yin goyo a babura masu kafa biyu

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta haramta yin goyo a babura masu kafa biyu a kananan hukumomin da ke kwaryar birnin Kano.
Hakan na cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa shafin sa na Facebook.
Sanarwar ta kuma jadddada dokar hana zirga zirgar baburan adai-daita sahu daga karfe 10 na dare zuwa wayewar gari.
Haka kuma, rundunar ta ce za ta hada hannu da sauran jami’an tsaro na Kano musamman na hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta KAROTA wajen kama duk wanda ya karya dokar.
Rundunar ta kuma jan hankalin mutane da su tabbatar da cewa sun bi dokar da aka sanya, domin magance duk wani ba ta gari a fadin jihar.
You must be logged in to post a comment Login