Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Rundunar yan sandan Kano ta sanya dokar takaita zirga-zirga daga 12:00 na daren Juma’a

Published

on

Rundundar ‘yan sandan jihar Kano, ta sanya dokar takaita zirga-zirgar jama’a da ababen hawa daga karfe 12:00 na daren yau juma’a 17 ga watan Maris.

Hakan na cikin wata sanarwa da Kwamishinan ‘yan sandan Kano Muhammad Hussain Gumel ya fitar a wani bangare na shirye-shiryen gudanar da zaben gwamna a gobe.

A cewar sanarwar, yanzu haka rundunar ta kammala duk wani shirinta domin tabbatar da tsaro a yayin zaben gwamna, ta hanyar hada kai da sauaran takwarorinta na tsaro don tabbatar da zaman lafiya.

Ya kuma ce, a yayin zaben an haramta sanya duk wata alamar jam’iyyar siyasa a wajen zabe, sannan an haramta wa kungiyar yan sintiri ta Vigilante da jami’an hukumar KAROTA shiga harkokin zabe a fadin jihar Kano.

Muhammad Gumel ya yi kira ga Al’ummar jihar Kano da su gaggauta bayar da rahoton duk wani motsi da ba su gamsu da shi ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!