Labarai
Rundunar yan Sandan Kano ta sha alwashin tabbatar da tsaro a makarantu

Rundunar yan sandan jihar Kano ta sha alwashi cigaba da tabbatar da tsaro a daukacin makarantun da ke jihar.
Kwamishinan rundunar Ibrahim Adamu Bakori, ne ya bayyana hakan yayin taron da aka shirya kan nasarorin da hukumar ke samu a bangaren tsaro.
Kwamishinan ya kuma ya yaba da kokarin jami’an rundunar tare da gargadin su da su kara kaimi wajen yin aiki cikin kwarewa da bin doka da kauce wa tsoma baki a shari’o’in farar hula da kuma gujewa cin hanci da rashawa.
Rundunar ta tabbatar da kudirinta na ci gaba da hadin gwiwa da bangarori daban-daban domin tabbatar da zaman lafiya da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.
You must be logged in to post a comment Login