Labarai
Rundunar Yan sandan kasar nan ta kori wasu jami’anta 3
Rundunar yan sandan kasar nan ta kori wasu jami’anta uku da ke ofishin yan sanda na Ijanikan a jihar Lagos bisa laifin yin fashi da makami ga wani dan kasar Togo mazaunin Najeria kimanin naira 221, 508
Wadanda aka korar sun hadar da Gbemunu Afolabi, da kuma Afolabi Oluwaseun, sai kuma Adingun Omotayo, inda rundunar ta ce an koresu ne sakamakon cin hanci da rashawa.
Tun a ranar Larabar da ta gabata ne aka samu rahoton cewa rundunar yan sandan ta kama wasu yan sanda hudu, bisa zargin yin fashi ga wani dan karsar Togo mazaunin kasar nan mai suna Theodore Ifunnaya, Sefa dubu 350 kwatankwacin naira 221,508.
Haka kuma rahotannin sun yi nunu da cewa korarrun yan sandan sun yiwa Theodore tsinke ne lokacin da yake shigowa kasar nan domin bikin kirsimeti da na sabuwar shekara, inda kuma suka azabtar dashi bayan kama shi.
A lokacin da yan sandan suka fahinci cewar matashin na dauke da kudaden ne ya sanya suka rufar masa, suka kuma kwace kudaden suka bashi naira dubu biyu domin ya yi kudin moto zuwa gida.