Connect with us

Kiwon Lafiya

Gwamnatin tarayya zata baiwa jihohi kudaden Paris club

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ce nan bada dadewa ba, za ta bai wa jihohi kason karshe na kudaden Paris Club da ya kai sama da naira biliyan dari shida da arba’in da tara.

Ministan kudi Zainab Ahmed ce ta bayyana haka yayin wani taron manema labarai jiya a Abuja

Ta ce tuni ma’aikatar kudi ta kammala aikin tantance kididdigar sauran kudaden da ya rage domin mayar da shi ga jihohi.

Da ta ke magana kan kasafin kudi kuwa, ministar cewa ta yi, tsakanin watan Yunin bara lokacin da shugaban kasa ya sa hannu kan kasafin kudin shekarar da ta gabata zuwa watan Mayun bana gwamnatin tarayya ta fitar da sama da naira tiriliyan biyu don gudanar da manyan ayyukan raya kasa a sassa daban-daban na kasar nan.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,749 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!