Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Rushe SARS : Wasu matasa na zanga-zanga a Kano

Published

on

Yanzu haka wasu matasa na tsaka da gudanar da zanga-zanga a birnin Kano kan goyon bayan sabon tsarin ‘yan sandan SWAT da  babban Sefeton ‘yan sanda ya ce za a samar bayan rushe SARS.

Masu zanga-zangar sun mamaye kofar fadar gwamnatin jihar Kano in da suke nuna goyan bayan su kan kafa sashen SWAT don yaki da fashi da makami wacce babban sefeton ‘yan sanda Muhammad Adamu zai kafa.

Sabuwar rundunar ta SWAT, wace ake kira da  Special Weapons and Tactics a harshen nasaranci a cewar babban sefeton ‘yan sanda za’a sake inganta ayyukan su da kuma basu horo na mussaman.

Wakiliyar mu Zara’u Nasir ta rawaito cewa masu zanga-zangar na dauke da katina da banoni dake nuna goyan bayan su kan SWAT.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!