Labarai
Tawagar G7 ta yi watsi da matakin jam’iyyar APC na Ƙasa
Saƙon na tawagar su Malam Shekarau zuwa ga shugaban riƙon jam’iyyar na ƙasa, wadda kuma suka aike wa Freedom Radio kwafi a cikin dare, sun fara ne da bayyana jawabi kamar haka.
Muna sanar muku da cewa mun karɓi wasiƙar da kuka aiko mai kwanan watan 7 ga Fabrairu na shekarar 2022, wadda aka aike wa jagoranmu Malam Ibrahim Shekarau.
Kazalika mun ji daɗi bisa yadda kuka nuna damuwarku kan halin da jam’iyyar APC ke ciki a Kano, tare da yunƙurinku na ganin an samu daidaito.
Muna fatan zaku tuna irin tattaunawar da bayanan da aka riƙa gabatarwa daga dukkan ɓangarorin domin ƙoƙarin ganin an samu daidaito.
Mun yi tsammanin cewa zamu ga takardarku ta mayar da hankali kan abubuwan da aka tattauna na shawarwari da matsaya daga kowane ɓangare ya bayar, kamar yadda aka cimma.
Amma kash! Abin takaici sai ga wannan takarda taku, ta saɓa da duk abin da kuka faɗa mana a zaman sulhu.
Wani abin takaicin ma shi ne yadda yanzu haka wannan takarda hadiman Gwamnatin Kano ke ta yaɗa ta a kafafen sada zumunta tare da cewar wai kun miƙa musu jam’iyyar ɗungurungum, a daidai lokacin da mu bata ma kai ga isowa gare mu ba.
Saboda waɗannan dalilai muna masu sanar da kai cewa, kwata-kwata bamu amince da wannan wasiƙa taka ba, mun kuma yi watsi da ita baki ɗaya.
Muna fatan sake inganta tsarin gudanar da jam’iyyarmu mai albaraka.
Haza Wasalam mun barka lafiya.
Saƙo daga Sanata Malam Ibrahim Shekarau da Sanata Barau Ibrahim Jibrin da kuma Tijjani Abdulƙadir Joɓe sai kuma Nasiru Abduwa Gabasawa, da kuma Barista Haruna Isah Dederi sai kuma Sha’aban Ibrahim Sharaɗa da kuma Alhaji Shehu Ɗalhatu.
You must be logged in to post a comment Login