ilimi
Sace daliban Kebbi hari ne kai tsaye ga makomar Najeriya- Ministar Mata

Ministar harkokin Mata Imaan Sulaiman Ibrahim, ta nemi a gaggauta sakin dalibai mata 25 na jihar Kebbi da aka sace, ta na mai bayyana lamarin a matsayin hari kai tsaye ga makomar Najeriya.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, Ministar ta ce, sace daliban ba wai kawai cin zarafin iyayensu ba ne, har ma yana nuna irin barazanar da ‘yan ta’adda ke yi wa ilimi da zaman lafiya a fadin Najeriya.
Ministar ta yi kira ga hukumomin tsaro da su ƙara matsa kaimi wajen ceto yaran cikin koshin lafiya tare da tabbatar da cewa irin wannan ta’addanci bai sake faruwa ba a ko’ina.
You must be logged in to post a comment Login