Labarai
Sabbin dokokin lafiya da Saudiyya ta sanya ta shafi dukkan maniyyata- NAHCON

Hukumar kula da aikin Hajji ta Najeriya NAHCON ta ce sabbin dokokin lafiya da kasar saudiyya ta saka akan masu niyyar zuwa aikin hajji na shekarar 2026, ya shafi kowacce kasa a duniya ba iya ‘yan Najeriya kadai ba.
Mai magana da yawun hukumar Hajiya Fatima Sanda Usara ce ta bayyana hakan ta cikin wani sakon murya da ta aiko wa Freedom Radio.
Hukumar ta NAHCON ta bayyana hakan ne a wani bangare na ci gaba da shirin tunkarar Ibadar aikin hajjin bana da ta ke yi a halin yanzu.
Haka kuma Hajiya Fatima Sanda Usara, ta bayyana cewa akwai tanadi na yin rigakafin cutar Corona watau covid-19 da sauran cututtuka ga kowanne maniyyaci a fadin duniya da hukumomin Saudiyyan za su yi.
You must be logged in to post a comment Login