Labaran Kano
Sabbin shugabannin Sakandaren Gwale Goba sun karbi aiki
Sababbin shugabannin tsofaffin daliban makarantar Gwale Secondary na kasa Goba sun kama aiki bayan karbar handing over da su ka yi.
Sabon shugaban Alhaji Mukhtar Diso ya yi alwashin kawo sauye sauye da aiki tukuru domin kawo cigaban da ya kamata a makarantar.
Ya kuma yi Kira ga ilahirin tsofaffin dalibai makarantar dake ko’ina a fadin kasarnan dama Duniya baki daya da su ci gaba da bayar da gudunmawar su a makarantar.
A nasa jawabin tsohon shugaban kungiyar, Engineer Hassan Abdulkadir ya ce “a shirye nake na cigaba da bawa makarantar Gwale gudunmawa a duk lokacin da aka neme”.
Ya kuma godewa sauran tsofaffin shugabannin makarantar Sakandaren ta Gwale bisa gudunmawar da Suka bada
You must be logged in to post a comment Login