Labarai
Sabon shugaban INEC ya sha alwashin kare dokokin zaɓe

Sabon shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya INEC, Joash Amupitan, ya yi alƙawarin kare dokokin zaɓe da na ƙundin tsarin mulki.
Amupitan ya ƙara da cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bashi umarnin c tabbatar da an yi zaɓe mai inganci a faɗin Najeriya.
Amupitan wanda ya bayyana hakan bayan rantsar da shi a ranar Alhamis a Abuja.
Sabon shugaban shi ne jagorar hukumar zaɓen ƙasar na shida tun bayan komawar ƙasar turbar dimokradiyya a shekarar 1999.
You must be logged in to post a comment Login