Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Sai tsofaffun ma’aikatan gidan jarida sun rinka tallafawa aikin-Rattawu

Published

on

Kungiyar ma’aikatan gidajan Radiyo da talabijin ta kasa RATTAWU, ta bukaci tsofaffun ma’aikatan gidajen jarida, da su rinka bayar da gudunmawar data da ce wajen kara inganta aikin a kasar nan.

Shugaban kungiyar a jihar Kano kwamred Abubakar Garba Maccido, ne ya bayyan hakan ya yin wata ziyara da kungiyar tsofaffun ma’aikatan gidan Talabijin na Abubakar Rimi dake kanon suka kai ofishin kungiyar a jiya Alhamis.

Maccido ya ce dole sai tsofaffun ma’aikatan da suka bar aiki a gidajan jaridu daban-daban dake ciki da wajen kasar nan sun rinka tallafawa aikin yadda ya kamata.

Ya kamata ‘yan jarida su samu yancin kawo rahoton wasanni ba tare da fargaba ba – CAF

Da yake jawabi shugaban kungiyar tsofaffun ma’aikatar gidan Talabijin na Abubakar Rimi dake nan Kano, Injiniya Usman Sa’idu cewa ya yi, a shirye kungiyar take ta bayar da kowacce irin gudunmmawa da za ta ciyar da aikin gaba a nan Kano dama Najeriya baki daya.

Injiniya Usman Sa’idu ya kuma ce makasudin kafa kungiyar shi ne domin tallafawa ‘ya’yan abobokan aikin su da suka rasu da wadan da basu dashi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!