Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

 Sakon Sabuwar shekara : PDP ta nemi ‘yan Najeriya su yi wa kasa addu’o’i

Published

on

Jam’iyyar PDP ta bukaci al’ummar Najeriya da su yiwa kasar addu’oin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali da samun bunkasa tattalin arziki a shekarar da muka shiga ta 2021.

Jamiyyar ta PDP ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa data fitar a daren jiya a birnin tarayya Abuja mai dauke da sa hannun sakataren ta Mr Kola Ologbondiyan.

Ologbondiyan ta cikin sanarwar ya kuma yabawa ‘yan Najeriya bisa jajir cewar da suke wajen addu’oi na samun zaman lafiya da kwanciyar hankali game da hare-haren da ake samu na yan bindiga da masu garkuwa da mutane a fadin kasar a shekarar data gaba ta 2020.

Ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su cigaba da nuna soyayya a tsakanin su ta hanyar rashin nuna kyama musamman nuna banbancin addini ko kabila.

Sanarwar ta kuma taya al’ummar ta Najeriya murnar shiga sabuwar shekara ta 2021 cikin nasara tare da samun nasarori ta kowanne bangare.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!