Labarai
Sallah : Yadda matan Kano suka cika gidajen yin kunshi da kitso
A ya yin da ake ci gaba da shirye-shiryen tunkarar bukukuwan babbar sallah suma mata ba’a barsu a baya ba, domin ana su bangaren suna ci gaba da shirye shiryensu musamman wajen yin kunshi da shirin yadda za suyi suyar nama.
Duk da kasancewar hukumomi nata kiraye-kiraye kan cewa jama’a su zauna a gidajensu, yayin bukukuwan sallah domin dakile cutar Corona a nasu bangaren mata iyaye na gida na ci gaba da shirye-shiryen tunkarar bikin na sallah.
Yayin da wasu ke zuwa gidan kunshi da kitso wasu kam siyan kayyakin kamshi da zasu gudanar da suyar nama suke.
Freedom rediyo ta tattauna da wasu mata kan yadda suke gudanar da shirye-shiryensu na sallah.
Haka zalika wasu mata da Freedom Radiyo ta iskesu a gidan kunshi sun bayyana cewa akwai cunkoso a mafi yawa na gidajen kitso da suka ziyarta.
Hajara Ya’u Haruna wata macece da ta ke sana’ar kunshi ta bayyana cewar cuta Corona ta yi mata illa sakamakon cewa ba ta samun abokan hulda kamar yadda ta ke samu a shekarun baya.
Wakiliyar mu Aisha Shehu Kabara ta rawaito cewa, Malama Hajara Ya’u ta kuma ce tun kimanin sallah saura sati daya ta ke gudanar da sana’ar ta kunshin
You must be logged in to post a comment Login