Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Nishadi

Salman Khan ya kwace wayar wani masoyinsa da ya dauki hoton selfie da shi

Published

on

Bisa al’ada ko wane Jarumi ya kan yi wasu ‘yan tafiye-tafiye a wani bangare na gudanar da aikin sabon fim.

Yanzu haka dai jarumin masana’antar shirya fina-finai ta Bollywood Salman KHAN yana tsaka da aikin wani sabon fim dinsa mai suna RADHE.

A yayin da Jarumi Salman Khan ya sauka a filin jirgin sama na Garin Goa dake yammacin kasar India, wani masoyin sa yayi yi yunkurin daukar hoto salfie da shi.

Sai dai an hangi jarumin cikin fushi ya kwace wayar masoyin nasa a dai-dai lokacin da ya karaso kusa da shi da nufin daukar hoton.

Ko a shekarar 2019 da ta gabata ma an zargin masu tsaron lafiyar jarumi Salman khan da kwace kyamarar wasu ‘yan jarida wadanda suka yi kokarin daukar sa a hoto, amma bai ce komai ba.

Sai dai duk wannnan dabi’a ta jarumi Salman khan masu sharhi na kallon sa a matsayin daya daga cikin jaruman Bollywood dake kaunar talakawa tare da tallafa musu.

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!