Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Samar da dangantaka mai kyau a jami’o’i zai kawo cigaba – Adamu Adamu

Published

on

Ministan ilimi Malam Adamu Adamu ya kaddamar da majalisar gudanarwa na jami’o’in kasar nan 13.

Malam Adamu Adamu ya kaddamar da majalisar ne a yau Litinin a babban birnin tarayya Abuja, yayin da ya bukace su da su samar da kyakyawan dangantaka a tsakanin su  lokacin da suke gudanar da ayyukan su cikin shekaru 4 da za su kwashe suna yi.

Ka zalika ya yi kira ga majalisar gudanarwar da su bi ka’idojin aiki yadda ya kamata ta amfani da dokokin da hukumar samar da ayyukan yi ta kasa ta yi.

A cewar ministan kamata ya yi majalisar ta bijiru da sababbin hanyoyin da gwamnatin tarayya zata samar da kudaden shiga.

Da yake jawabi babban sakatare na hukumar kula da jami’o’I ta kasa farfesa Abubakar Rasheed ya ce kaddamar da majalisar a halin yanzu kamar an dasa danba ne wajen samar da kwarewa a jami’o’I 12 na Najeriya

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!