Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Dalibai 2,700 a Jigawa sun rubuta jarabawar neman gurbin tafiya karatun Likita

Published

on

Dalibai 2,700 ne suka zana jarabawar farko ta neman samun damar tafiya karatun zama likita kasashen Ketare , wadda gwamnatin jihar Jigawa ta shirya don zabar dalibai 60 daga ciki.

Hakan na zuwa ne bisa karkashin daukar nauyin karatun su zuwa kasar Sin (China ) a karkashin shirin da Gwamnatin jihar ta bullo dashi ga yayan Marasa galihu.

Labarai masu Alaka.

Kungiyar KASSOSA ta gudanar da taronta na shekara a jihar Jigawa

Ma’aikatan lafiya sun kamu da Corona a Jigawa

Kwamishinan Lafiyar jihar Jigawa Dr. Abba Zakari ne ya bayyana haka ga manema Labarai a Dutse, ya yin gudanar da jarabawar da daliban suka yi, a makarantar Koyon Mulki da kasuwanci dake Dutse wato Jigawa State Polytechnic, a ranar litinin din nan.

Wakilinmu Muhd Aminu Umar Shuwajo daga Dutsen jihar Jigawa , ya ruwaito  cewar bayan tantance wanda suka samu Nasara , dalibai 60 ake sa ran zasu ci moriyar tallafin Karatun .

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!