Labarai
Samar da kungiyoyin wanzar da zaman lafiya zai taimakawa tsaro a cikin al’umma: Dagaci
Daya daga cikin mai rike da sarautar gargajiya a Jihar Kano ya bayyana cewa Samar da kungiyar da zata rinka wanzar da zaman lafiya a unguwanni zai taimaka wajen kawar da barazanar tsaro a Jihar.
Fagaci Kano Alhaji Muhammad Sayyadi Nura ne ya bayyana hakan yayin bikin kaddamar da wata kungiyar wanzar da zaman lafiya a Kano mai suna sharada industrial peace Club a ranar Asabar.
Alhaji Muhammad Sayyadi Nura ya ce ‘duba da karancin jamian tsaro da ake gama dasu a Jihar da kasar baki daya, irin wadannan kungiyoyi zasu taimaka wajen samar da tsaro a cikin al’umma’.
A nasa bangaren dagacin unguwar sharada Alhaji Ilyasu Muazu Sharada cewa ‘sun kafa wannan kungiyar ne don samar da zaman lafiya tsakanin Kamfanonin dake wadannan shiyoyin da suka Hadar da Sharada da Ja’in da Zawa ciki da alummar da ke zauna a unguwannin’.
A nata bangaren Hadiza Bashir Buhari wacce daya ce daga cikin wata kungiyar ta wanzar da zaman lafiya a Kano cewa tayi ‘ kafa kungiya irin wannan zai taimaka wajen dakile duk wata fitina daka iya tasowa tsakanin ma’aikatan Kamfanonin da mazauna unguwannin’.
Freedom Radio ta rawaito cewa ‘Kungiyar sa kai dake wanzar da zaman lafiya ta CIPP ce ta sauki nauyin taron, karkashin jagorancin USAID’.
You must be logged in to post a comment Login