Kasuwanci
Samar da masana’antu a Arewacin ƙasar nan zai bai wa matasa ayyukan yi – Farfesa Murtala Sagagi
Masanin tattalin arziki a makarantar koyar da harkokin kasuwanci a jami’ar Bayero anan Kano ya ce, samar da wadatattun masana’antu a Arewacin ƙasar nan rage marasa aikin yi.
Farfesan Murtala Sabo Sagagi ya ce, yin hakan zai taimaka wajen rage matasan da ke zaune babu abin yi a yanzu.
Farfesan Sagagi ya bayyana hakan jim kaɗan bayan kammala shirin “Barka da Hantsi”na nan Freedom Radio.
Ya ce, idan har ana son samar da yanayi mai kyau a kasar nan, to kuwa sai gwamnati ta gyara tsarin masana’antu da harkokin tafiyar da su.
Murtala Sabo Sagagi Ya ƙara da cewa idan da gwamnati za ta riƙa ciyo bashi tana sakawa cikin masana’antu to kuwa yankin Arewa zai zarce kudancin ƙasar nan.
You must be logged in to post a comment Login