Connect with us

Kiwon Lafiya

Sanata Bukola Saraki ya musanta zargin da ake yada na neman shugabanci kasa

Published

on

Shugaban Majalisar Dattijai Sanata Bukola Saraki ya musanta zargin da ake yadawa a wasu kafafan yada labarai cewa wai zai nemi takarar shugabancin kasar nan a kakar zabe mai zuwa ta badi.

Cikin zantawarsa da manema labarai mashawarcin shugaban Majalisar Dattijan kan harkokin yada labarai Yusuph Olaniyonu ya ce zancen ba shi da tushe balle mafari.

Cikin wasu rahotannin da aka yada an nuna cewa Bukola Saraki zai nemi mataimakinsa na Majalisar kuma dan jam’iyyar PDP wato Sanata Ike Ekweremadu ya tsaya masa a matsayin dantakarar mataimakin shugaban kasa.

A shekarar 2011 Bukola Saraki ya nuna bukatarsa ta neman takarar shugabancin kasar nan a Jam’iyyar PDP, mma daga bisani ya janyewa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!