Labarai
Sanata Natasha ta gayyaci Akpabio da takwarorinta domin buɗe aiki a mazaɓarta

Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan mai wakiltar Kogi ta Tsakiya ta gayyaci Shugaban Najalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, da sauran ’yan majalisa zuwa bikin kaddamar da ayyukan raya kasa a mazabarta ta Jihar Kogi.
Sanata Natasha ta bayyana hakan ne a shafinta na Facebook, inda ta ce gayyatar ta zo ne yayin cikar ta shekaru biyu a matsayin sanata duk da kalubalen da ta fuskanta, ciki har da dakatarwa, barazanar rayuwa, da ƙoƙarin cire ta daga kujerarta.
Bikin kaddamar da ayyukan, wanda ya haɗa da bude muhimman gine-gine da rabon tallafi, zai gudana ne a ƙaramar hukumar Okene, ranar Lahadi 2 ga Nuwamba, shekarar 2025.
You must be logged in to post a comment Login