Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Sanatocin Zamfara 3 sun sauya sheƙa daga PDP zuwa APC

Published

on

Sanatocin jam’iyyar PDP guda hudu sun sanar da sauyin sheka daga jam’iyyar adawa ta PDP zuwa jam’iyya mai mulki ta APC, a yayin zaman majalisar na yau laraba.

Sanatocin sun hada da guda uku daga jihar Zamfara, wadanda suka hada da Sahabi Alhaji Ya’u, mai wakiltar mazabar Zamfara ta arewa da  Hassan Muhammed daga Zamfara ta tsakiya, sai kuma Lawali Hassan Anka daga Zamfara ta yamma.

Haka zalika shima sanata mai wakiltar mazabar Delta ta arewa, Peter Nwaoboshi ya sanar da ficewar sa daga jam’iyyar ta PDP zuwa APC.

Shugaban majalisar dattijai sanata Ahmed Lawan shine ya karanta wasikar sauyin shekar sanatocin guda hudu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!