Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Zan bibiyi kasafin bana don tabbatar da ba a canja shi ba- Ndume

Published

on

Dan majalisar dattawa mai wakiltar Borno ta kudu sanata Ali Ndume ya ce ba zai taba zuba ido ya ga an sauya wani abu daga kasafin kudin da aka warewa yankin arewacin kasarnan ba.

Sanata Ali Ndume ya bayyana hakan ne a wata hira da ‘yan Jarida, inda ya ce tuni ya gayyato wani kwararre kan kasafin kudi domin bibiyar kasafin kudin na bana don gane ko akwai gibin da aka yiwa yankin arewacin kasarnan.

Kazalika ya kalubalancin kudirin gwamnatin tarayya na sauya matsugunnin wasu manyan bangarori na Babban bankin Nigeria CBN da kuma hukumar lura da tasoshin jiragen saman kasarnan daga birnin tarayya Abuja zuwa Legas, yana mai cewa dalilan da aka bayar na daukar matakin basu da tushe bare makama

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!