Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Sarakuna na da gudin mawar bayarwa wajen yakar Corona-Jigawa

Published

on

Gwamnatin jihar Jigawa ta ce, sarakunan gargajiya na cikin wadanda za su taimakawa gwamnati wajen sanya idanu akan iyakokinta da makwabtan jihohi da aka samu bullar cutar corona.

Gwamnan jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar ne ya bayyana haka yayin ganawa da ya gudanar da sarakunan gargajiya da kuma shugabannin addinai a gidan gwamnati da ke Dutse babban birnin jihar.

Ya ce, sarakunan za su taimaka ne wajen kula da iyakokinta da jihohin Kano da Bauchi da kuma Katsina wadanda aka samu bullar cutar covid-19 a cikinsu.

Muhammad Badaru Abubakar ya kuma ce, an cimma yarjejeniya cewa sarakunan za su umarci hakimai da dagatai da masu unguwanni da su rika aiki tare da jami’an tsaro wajen kula da kan iyakokin kasar.

Gwamnan na jihar Jigawa ya kara da cewa, kowane dan jihar yana da damar sanar da jami’an tsaro matukar sun ga wani bakon mutum ya shigo jihar ta barauniyar hanya daga makwabtan jihohi.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!