Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Abubuwa bakwai da sarkin Kano ya fada kan Lockdown

Published

on

A yau juma’a ne ya kasance rana ta farko da aka fara zaman gida na tsawon mako guda da gwmnatin Kano ta umarci yi a wani yunkuri da take na dakile yaduwar annobar Corona a Kano.

inda mai mai martaba sarkin Kano Aminu Ado Bayero ya gabatar da wani jawabi na musamman ga manema labarai game da zaman gida da al’ummar Kano suka fara.

Daga cikin muhimman bayanin sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya gabatar ga al’umar Kano a yau sun hadar da.

Abu na farko sarkin ya bayyana jimaminsa bisa halin da masu karamin karfi za su shiga wajan neman abincin da za su ci a wannan yanayi da aka shiga.

Sannan yayi kira ga gwamnati da ta samar da hanyoyin tallafawa masu rauni, domin rage musu radadin halin da suke ciki.

Har ila yau, Sarki Aminu Ado Bayero ya tunatar da mutane kan yadda annoba ta samo asali tun daga zamanin sahabbai, a don haka ya kara jan hankalin al’umma kan yadda da kaddara.

Ya kuma ce komawa ga Allah zai taimaka gaya wajan samun saukin halin da aka tsinci kai a ciki, na annobar ta Corona.

ya kuma ja hankalin mutane da su mayar da hankali wajan tuba ga Allah da neman rahamarsa, don samun saukin annobar ta Corona.

Aminu Ado Bayero ya kuma ce matakan da gwamnati ta dauka misalai ne wajan dakile yaduwar cutar Corona a cikin al’umma.

Ya kuma roki muta ne da su gudar da ibadunsu a gidajen su don gujewa yaduwar cutar Covid- 19.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!