Addini
Sarki Sanusi II ya bukaci a dawo da tsarin Amirul Hajji

Mai martaba Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sunusi II, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta duba yiwuwar dawo da Amirul hajji da zai jagoranci maniyata aiki hajji duba da irin muhimmanci da ya ke da dashi a tsarin koyarwar addinin Musulunci.
Sarkin ya yi wannan kira ne lokacin da ya ke karbar bakuncin shugaban hukumar jindadin alhazai ta Kano Alhaji Lamin Rabi’u Dan Baffa tare da jami’an hukumar yayin da suka kai ziyara fadarsa.
Khalifa Muhammadu Sunusi II, Wanda ya yi jawabi mai tsawo dangane da muhimmancin dawo da Amirul hajji ta fuskar samar da gyara da daidaita tsarin gudanar da jagorancin aiki hajji.
A nasa jawabin shugaban hukumar jin dadin alhazai ta Kano Lamin Rabi’u Dan Baffa, ya bayyana cewa sun kai ziyarar ne don gaisuwar ban-girma tare da shaida wa sarkin irin ci gaban da aka samu a fannin.
You must be logged in to post a comment Login