Connect with us

Labarai

Sarki Sunusi zai gudanar da hawan Sallah – Gwamnatin Kano

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta sanar da al’umma cewa ta samu sahihan bayanan sirri daga Majalisar Tsaro ta Jiha, da ke nuna cewa akwai wasu mutane da ke ƙoƙarin haddasa rikice-rikice da tayar da zaune tsaye a lokacin bukukuwan Eid-el-Fitr (Sallah) da ke tafe.

 

A sanarwar da Kwaminan yada labarai Comr. Ibrahim Abdullahi Waiya ya fitar ya ce gwamnatin ta jaddada cewa duk da ƙoƙarinta na kare da bunƙasa al’adun gargajiya na Kano, ba za ta lamunci duk wani abu da zai kawo cikas ga zaman lafiya da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma ba.

 

Bayan tattaunawa da Majalisar Masarautar Kano da sauran masu ruwa da tsaki, gwamnati ta amince da waɗannan tsare-tsare:

 

Hawan Idi: Za a gudanar da shi karkashin jagorancin Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II, daga filin Idi na Kofar Mata, ta hanyoyin da aka tsara, har zuwa Gidan Shettima, sannan a ƙare a Kofar Fatalwa ta Fadar Sarkin Kano.

 

Hawan Nasarawa: Za a gudanar da shi a wani salo na musamman, amma ba tare da hawa dawakai ba.

 

Hawan Daushe: An dakatar da shi a wannan lokaci, kuma za a mayar da shi zuwa wasu bukukuwan Sallah na gaba, in Allah ya yarda.

 

Hawan Fanisau da Hawan Dorayi: Su ma an dakatar da su na ɗan lokaci domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro.

 

Gwamnatin ta umarci dukkan hukumomin tsaro da su ƙara zage damtse wajen sa ido, tare da tabbatar da bin waɗannan umarni, da kuma ɗaukar duk matakan doka don hana duk wani tashin hankali kafin, lokacin, da bayan Sallah.

 

Haka kuma, gwamnati ta buƙaci al’umma da su kasance masu bin doka, su ba hukumomin tsaro haɗin kai, su guji yaɗa jita-jita, tare da gudanar da harkokinsu cikin lumana a duk lokacin bukukuwan Sallah.

 

Gwamnatin Jihar Kano ta gode wa jami’an tsaro bisa jajircewarsu wajen tabbatar da zaman lafiya, tare da tabbatar da cewa za ta ci gaba da aiki don ganin an gudanar da bukukuwan cikin kwanciyar hankali.

 

A ƙarshe, gwamnati ta taya dukkan Musulmi murnar zagayowar Eid-el-Fitr, tare da fatan a yi Sallah lafiya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!