Labarai
Sarkin Kano ya nada sabon Dagacin garin Ganduje

Mai martaba sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sunusi II, ya nada Malam Jamilu Sani Umar a matsayin sabon dagacin garin Ganduje da ke karamar hukumar Dawakin Tofa da kuma dagacin garin burji a karamar hukumar doguwa Dakta Musa Garba Usman.
Wazirin Kano Alhaji Sa’ad Shehu Gidado, wanda ya yi magana a madadin Sarki, ya hori Dagatan da su mayar da hankali wajen kula da lafiyar al’ummar yankunan su da kuma sanya idanu kan bakin da suke shigowa yankunan su ba tare da izini ba.
A nasu jawaban daban-daban, dagatan sun gode wa Mai martaba sarkin bisa nadin nasu.
Haka kuma, Sakin ya karbi bakuncin daliban jami’ar gwamnatin tarayya da ke Dutse a jihar jigawa bisa jagorancin shugaban dalibai na jami’ar Muhammad Muhammad Zakari.
You must be logged in to post a comment Login