Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Sarkin Kano ya yaba wa ƙungiyar matan ƴan sanda

Published

on

Mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ya buƙaci ƙungiyar matan ƴan sandan Nijeriya da su ƙara himmatuwa wajen haɗa kan mambobinsu musamman na jihar Kano domin koya wa marayu da masu bukata ta musamman sana’oin dogaro da kai.

Sarkin ya buƙaci hakan ne lokacin da tawagar kungiyar matan ƴan sandan jihar Kano watau Police Officers Wives Association, ƙarƙashin jagorancin Hajiya Aisha Muhd Hussain Gumel suka masa ziyara a fadarsa.

Alhaji Aminu Ado Bayero ya kuma bayyana jin daɗi bisa ziyarar tare da bayyana farin ciki bisa yadda matan suka kafa ƙungiyar don taimaka wa marayu saboda su dogara da kansu ba sai gwamnati ta basu aikin yi ba.

A nata jawabin Hajiya Aisha Muhd Hussain Gumel ta bayyana cewa sun ziyarci fadar Sarkin ne domin nuna goyon bayansu ga masarautar da kuma buƙatar basu shawarwari na ciyar da ƙungiyar gaba.

 

Rahoton: Shamsu Da’u Abdullahi

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!