Labarai
Sarkin Kano ya yi alwashin taimaka wa gwamnatin tarayya da jami’an tsaro don magance rikicin sassan Arewa
Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu yayi alwashin taimakawa gwamnatin tarayya da jami’an tsaro wajen ganin an magance rikicin al’umma da yake faruwa a wasu sassan Arewacin kasar nan da nufin samar da dauwamammen zaman lafiya a.
Muhammadu Sanusi na biyu ya bayyana hakan ne a wajen bikin tunawa da shahararren malamin addinin musulunci Gwani Mukhtar da aka gudanar a gidan Mambayya dake Gwammaja.
Sarkin ya ce akwai bukatar shugabannin kasar nan su maida hankali wajen ganin an yi adalci a irin rikice-rikicen al’umma dake faruwa a wasu sassan Arewacin Najeriya.
Muhammadu Sanusi na biyu ya kuma kara da cewa, irin tashin-tashina na rashin zaman lafiya da rashin kwanciyar hankali yake faruwa a wasu garuruwan Arewacin kasar nan ba abu bane da shugabanni za su zuba ido ,ba tare da daukar matakan gaggawa na magance matsalolin ba.
A nasa bangaren, shugaban kungiyar Kautal Hore Miyetti Allah, Bello Abdullahi Bodejo nuna damuwar sa ya yi dangane da rikicin makiyaya da manoma na jihar Benue, inda yake cewa makiyaya mutane ne masu kaunar zaman lafiya a inda suke.