Connect with us

Labarai

Sarkin Kano ya yi alwashin taimaka wa gwamnatin tarayya da jami’an tsaro don magance rikicin sassan Arewa

Published

on

Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu yayi alwashin taimakawa gwamnatin tarayya da jami’an tsaro wajen ganin an magance rikicin al’umma da yake faruwa a wasu sassan Arewacin kasar nan da nufin samar da dauwamammen zaman lafiya a.

Muhammadu Sanusi na biyu ya bayyana hakan ne a wajen bikin tunawa da shahararren malamin addinin musulunci Gwani Mukhtar da  aka gudanar a gidan Mambayya dake Gwammaja.

Sarkin ya ce akwai bukatar shugabannin kasar nan su maida hankali wajen ganin an yi adalci a irin rikice-rikicen al’umma dake faruwa a wasu sassan Arewacin Najeriya.

Muhammadu Sanusi na biyu ya kuma kara da cewa, irin tashin-tashina na rashin zaman lafiya da rashin kwanciyar hankali yake faruwa a wasu garuruwan Arewacin kasar nan ba abu bane da shugabanni za su zuba ido ,ba tare da daukar matakan gaggawa na magance matsalolin ba.

A nasa bangaren, shugaban kungiyar Kautal Hore Miyetti Allah, Bello Abdullahi Bodejo nuna damuwar sa ya yi dangane da rikicin makiyaya da manoma na jihar Benue, inda yake cewa makiyaya mutane ne masu kaunar zaman lafiya a inda suke.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,734 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!