Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Sarkin Kano ya ziyarci mutanen da suka ƙone a gobarar Masallaci

Published

on

Mai Martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ya kai ziyara asibitin Murtala domin duba marasa lafiya waɗanda wani matashi ya banka wa wuta a masallaci a dai-dai lokacin da suke gabatar da sallar Asubahi a garin Gadam da ke Larabar Abasawa a karamar hukumar Gezawa.

Sarki Alhaji Aminu Ado Bayero, Bayan nuna jimami da alhinin bisa iftila’in ya kuma yi addu’a da fatan samun lafiya ga waɗanda ke kwance a asibitin sakamakon wannan lamari da kuma fatan kiyaye afkuwar hakan a gaba.

Sarkin na Kano, ya kuma yi addu’ar Allah ya gafarta wa waɗanda suka rasu ya, sanya Aljanna ce makoma a garesu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!