Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Sarkin Kano ya gana da masu zuba jari daga kasar Sin

Published

on

A matsayin sa na jagora wajen kawo sauyi a tattalin arziki da kokari kan bunkasa masa’an tun a jihar Kano  Sarkin Kano Muhamma Sunusi na II zai karbi bakwancin masu zuba jari daga kasar China da safiyar yau a fadar sa dake kofar Kudu, a nan Kano.

Sai dai ajiya Alhmais ne Muhammadu Sunusi na II CON  a matsayin sa na shugaban kwamitin bada shawarwari kan zuba jari ya gana da masu wakiltar manyan kamfanonin biyar dake  sha’awar zuba jari daga kasar China a fadar sa.

Ganawar ta sami wakilai daga bankin raya masana’antu da bankin bunkasa kasashen Afrika da masu zuba jari daga nan Kano.

Ganduje da Sarkin Kano sun gana da masu zuba jari daga kasar China

Sarkin Karaye ya rushe majalisar masarautar sa

Tarihin zikirin shekara da ake yi a fadar sarkin Kano

Zulum- ya baiwa malamai 30 kwangilar addu’o’i a kasa mai tsarki

 

Bayan kamala ganawar ne, masu ruwa da tsaki daban-daban suka sanya hannun yarjiniya  da Bankin raya masana’atu da na bunkasa kasashen Afrika.

Haka zalika, wasu daga cikin wakilai daga kasar China wanda gwamnan yankin Shangdon ke jagoranta da kuma wasu wakilai na jam’iyyar Kwamunasanci sun iso nan Kano a wata ziyara ta kwanaki biyu wanda shima za su gana da gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na II da sauran kososhin gwamnati, da ‘yan kasuwa don samar da damamaki kan kasuwanci a nan Kano

Wakilan dai za su bar jihar Kano a ranar Asabar 9 ga wannan watan na Nuwanba.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!