Connect with us

Labarai

SARS: Ganduje ya dakatar da Salihu Yakasai

Published

on

Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya dakatar da mai bashi shawara na musamman kan yaɗa labarai Salihu Tanko Yakasai daga muƙaminsa.

Kwamishinan yaɗa labaran Kano Malam Muhammad Garba ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar.

An dakatar da Salihu Yakasai saboda bayyana wasu kalaman suka game da gwamnatin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a cewar sanarwar.

Kafin dakatarwar dai Salihu Yakasai ya soki manufofin gwamnatin tarayya a shafinsa na Twitter.

Salihu Yakasai ya soki shugaba Buhari da ƙin yin magana kan koken da ƴan Najeriya ke yi game da ƴan sandan SARS.

Ko a ranar 18 ga watan Afrilun da ya gabata, gwamna Ganduje ya sauke kwamishinan ayyuka na jihar Injiniya Mu’azu Magaji Ɗan Sarauniya sakamakon wasu rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Ɗan Sarauniya ya wallafa bayanai dake nuna suka ga shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa marigayi Malam Abba Kyari.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!