Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Aikin Allah: Hisbah ta yi rabon tallafi

Published

on

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta raba kayan tallafi ga marasa lafiya a asibitin Bamalli Nuhu da ke kofar Nassarawa.

Babban kwamandan hukumar Sheikh Muhammad Harun Ibn Sina ne ya jagoranci raba tallafin ga marasa lafiya a yau.
Ya ce, tallafin zai ragewa marasa lafiya radadin halin da suke ciki musamman a wannan lokaci da ake fuskantar matsin rayuwa.

Da take karbar tallafin a madadin shugabar asibitin Dakta Halima Ibrahim Magashi ta bukaci kungiyoyi da daidaikun al’umma da su ci gaba da tallafawa marasa lafiya a koyaushe.

Wakilinmu Muhammad Harisu Kofar Nassarawa ya rawaito cewa, marasa lafiya da dama ne suka samu tallafin tare da bayyana farin cikin su, bisa kayan da aka basu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!